Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shekaru 67 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Nuwamban-1954 Aka kafa dakarun kwatar 'yencin kasar Algeria karkashin jagorancin Ahmad Bin Billa, da haka kuma aka fara gwagwarmayar neman samun 'yencin kai na kasar Algeriya.
Tun a farkon karni na 19 miladiyya ne sojojin kasar Faransa suka mamaye kasar Algeria, sannan dukkanin yunkurin da mutanen kasar suka yi ta yi a tsawon shekaru 132 ya ci tura.
Amma daga karshe turawan sun bawa kasar yancin kai a shekara 1962.
Sannan Ahmad Bin Billah ya zama shugaban kasar Algeriya na farko bayan samun 'yencin kai. Sai kuma a shekara ta 1965 aka yi masa juyin mulki.
Ana daukar Ranar kafa dakarun kwatar 'yancin kasar Algeriya, a matsayin kasa a hukumance.
342/